Ina da goyon bayan dukkan sojoji - in ji sabon jagoran Mali

Sojin Mali Hakkin mallakar hoto
Image caption Sabon shugaba ya ce ba ya tsoron juyin mulki

Sojan da ya jagoranci juyin mulki a Mali ya shaida wa BBC cewa shi ke da iko da baki dayan kasar.

Kyaftin Amadou Sanogo ya ce baya tsoran wasu sojojin su yi masa juyin mulkin

Kyaftin Sanogo ya ce, “In da na yi ne ba tare da kwarin gwiwa da girmamawa da kuma matsayin da sojojin suka nuna min ba, to ai shi ne zan yi wannan fargabar, amma ai su ne suka dora ni kan wannan matsayin.”

Sai dai kuma wani wakilin BBC da ke yankin ya ce ba a tabbatar da irin goyan bayan da Kyaftin din ke da shi ba daga wajen manyan kwamandojin sojin kasar.

Yanzu haka 'yan tawayen Abzinawa sun yi amfani da halin da ake ciki suna rike da arewacin kasar ta Mali, amma Kyaftin Sanogo ya ce zai tattaunawar zaman lafiya tare da su.

Gabanin wannan, jagoran sojojin da suka yi juyin mulki a Mali, Kyaftin Amadou Sanogo, ya bayyana a gidan talabijin na kasar domin karyata jita-jitar da ake bazawa ta cewa an kashe shi

A jawabinsa y ace ne, “Barkanku da yamma jama'ar Mali. Barka da yamma 'yan uwana sojoji.

“Kyaftin Sanogo ne ke magana. Ina cikin koshin lafiya, komai lafiya lau.”

Kaptin Amadou Sanogo ya yi Allah wadai da kwasar ganimar da ta biyo bayan juyin mulkin.

Ya ce yana da shaidar cewa ba ainahin sojoji ba ne suka yi ta kwasar ganimar.

Wasu da suka yi shigar burtu ne da ke son ja wa wadanda suka jagoranci juyin mulkin bakin jini.

Wani dan jarida a birnin Bamako da ya yi hira da Kyaftin Sanogo ya shaida wa BBC cewa ga yadda ya ga Kyaftin Sanogon, hankalinsa a kwance yake.

Karin bayani