Kofi Annan ya samu goyon bayan Russia a kan rikicin Syria

Kofi Annan da Shugaba Medevedev Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dama ta karshe ta kauce wa yakin basasa a Syria?

Shugaban kasar Rasha ya yi gargadin cewa zuwan wakilin Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar kasashen Larabawa Syria, wato Kofi Annan, na iya kasancewa dama ta karshe ta kauce wa yakin basasa a kasar.

Dmitri Medved yana magana ne a Moscow a lokacin tattaunawarsa da Mr Annan, wanda ke son Rasha - wata babbar aminiyar Syria - ta dauki kwakwkwaran matsayi a kan shugaba Bashar al-Assad.

Shugaba Medvedev ya ce zamu ba da cikakken goyan bayan a kowane mataki da kuma duk abin da Rasha za ta iya yi.

Mr Annan ya yi marhabin da tayin cikakken goyan bayan da Rasah ta ba aikin da yake yi.

Har ma ya kwatanta hakan a matsayin wata dama ta kawo karshen rikicin Syria.

Ya kuma kara da yin kira ga Syriar da ta ba da damar kai agaji wuraren da rikicin ya fi kazanta.

Karin bayani