Obama ya gargadi Korea ta Arewa a kan harba tauraron dan-adam

Shugaba Obama
Image caption Ana jiran ganin abin da Korea ta Arewa za ta yi

Shugaba Obama ya gargadi Korea ta Arewa cewa za ta iya fuskantar yiwuwar kakaba mata takunkumi muddin ta ci gaba da shirye-shiryenta na harba wani kumbo zuwa sararin samaniya a watan gobe.

Da yake magana a Seoul tare da takwaran aikinsa na Korea ta Kudu, Lee Myung-Bak, Mr Obama ya ce zai yi wuya Amurka ta ci gaba da ba ta taimakon abinci muddin Pyongyang ta harba kumbon.

Ta wani tabaron hangen nesa ne dai a kan iyaka ta soji tsakanin Koreyoyin guda biyu, a karon farko Shugaba Obama ya ga Kore ta Arewa.

Wato dai kasa mai makaman nukiliya, da sabon shugaba matashi, Kim Jong-Un - wata kuma a halin yanzu take kallon kuda tare da Amurkar a kan shirin da take da shi na kaddamar da wani taron tauraron dan adam a watan gobe.

A taron manema labarai na hadin guiwa tare da takwararn aikinsa na Kore ta Kudu 'yan sa'o'i daga baya, Mr Obama ya ce kaddamar da kumbon da Kore ta Arewar za ta ya keta nauyin kasa da kasa da ke kan Korear ta Arewa.

Kuma tuni mutane suka shiga shakku a kan kamun ludayin sabon shugaban kasar.

Ya ce, "Ina ganin da wuya a fahimci Kim Jong-Un, a wani bangaren, saboda har yanzu komai bai daidaita ba a Korear ta Arewa.

"Har yanzu babu tabbas a kan wanene ke gudanar da al'amurra, da kuma ko mice ce manufarsu ta dogon lokaci."

A watan jiya ne dai Korea ta Arewar ta amince ta dakatar da wasu gwaje-gwajen makamai masu lizzami da ayyukan nukiliya, inda ita kuma Amurka za ta saka mata da ba ta agajin abinci.

Ita ma dai Majalisar Dinkin Duniya ta haramta wa Korea ta Arewar yin irin wadannan gwaje-gwaje.

Kore ta Arewar ta ce kaddamar da tauraron dan Adam batu ne na daban.

Ita kuma Amurka ta ce za fake da hakan ne a yi gwajin makami mai lizzami na dogon zango.

Wannan badakala dai ta dusashe taron koli a kan nukiliya na makon gobe, duk kuwa da cewa Kore ta Arewa ba ta cikin taron, kuma batunta bai cikin batutuwan da za a tattauna.

Karin bayani