An kashe a kalla mutane hamsin a Syria

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wani dan adawa a lardin Idlip

Masu fafutukar kafa demokradiyya a Syria sun ce an kashe a kalla mutane hamsin da hudu a ranar assabat, a fadan baya-bayan nan da aka gwabza tsakanin jami'an tsaro da masu bore.

An kuma ba da rahoton kisan wasu mutanen ashirin da biyar a Homs birni na ukku mafi girma a kasar.

An ce wasu mutanen akalla sun rasa rayukkan su a lardin Idlib dake arewa maso yammacin kasar da wasu goma a garin Saraqeb wanda jami'an tsaro suka afkaa ma.

Tun farko a jiya da rana, wakilin musamman na Larabawa da Majalisar Dinkin Duniya a Syria Kofi Anana ya isa Moscow don neman goyon baya ga shirin sa na neman zaman lafiya.