Amurka da Rasha za su rage makaman nukiliya

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaba Obama na Amurka

Shugaban Amurka Barrack Obama ya ce kasar sa za ta yi aiki da kasar Rasha ta fuskar kara rage makamansu na Nukiliya.

Lokacin da yake magana gabanin taron kolin da aka shiriya na tsaron nukiliya a Korea ta Kudu, ya ce abu ne mai yiwuwa ga kasar ta Amurka ta ci gaba da makaman kariya daga harin na nukiliya

Mista Obama ya ce a lokaci guda kasar za ta rage yawan makaman na ta na nukiliya.

Nan gaba dai Shugabanni daga kasashe sama da hamsin za su hadu da Mr Obaman a taron kolin kan sha'anin tsaron nukiliyar.