Ana bukatar karin miliyoyin daloli a Nijar

Matan Nijar
Image caption Mata da yara a Nijar na fama da wahala sakamakon karancin abinci

Kungiyoyin agaji na kasa-da-kasa sun ce ana bukatar karin miliyoyin daloli don tunkarar karancin abinci a Nijar, kafin matsalar ta zama wani babban bala'i.

A cewar kungiyoyin, kimanin mutane miliyan shida ne ke cikin mawuyacin hali a kasar ta Nijar saboda tsadar abinci da kuma kwararowar 'yan gudun hijira.

Shugaban hukumar agaji ta Save the Children, Justin Forsyth ya ce yawan yaran da ke fama da tamowa na karuwa.

"Saboda haka ya kamata mu kai dauki cikin gaggawa. Kuma ya kamata mu agazawa wadanda suka rasa kashi tamanin cikin dari na amfanin gonarsu saboda fari; lokaci na kurewa don haka ya kamata mu yi wani abu cikin gaggawa", in ji Mista Forsyth.

An dai kiyasta cewa a yankin Sahel mutane miliyan goma sha biyar da rabi ne yunwa ke yi wa barazana.

Abubuwa da yawa ne suka janyo hakan—kamar rashin isasshen ruwan sama, da hauhawar farashin kayayyakin abinci, da kuma dubban mutanen da suka koma yankin na Sahel sakamakon rikicin Libiya da na Cote d'Ivoire.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Karin bayani