An yaba da zaben Senegal

Masu zabe a Senegal Hakkin mallakar hoto x
Image caption Masu zabe a Senegal

Yanzu haka dai hankula sun kwanta a kasar Senegal, bayan da aka gudanar da zaben shugaban kasa cikin kwanciyar hankali ranar Lahadi.

Kungiyar Tarayyar Afrika da kasar Faransa, wadda ta yiwa kasar mulkin mallaka, sun yaba da yadda aka yi zaben—bisa ga dukkan alamu Macky Sall ya lashe zaben ne da gagarumar nasara a kan shugaba mai ci Abdoulaye Wade, mai shekaru tamanin da biyar, wanda kuma yunkurinsa na yin tazarce wajen neman wa'adin mulki na uku ya janyo mummunar zanga zanga.

Bayan sun kwashe daren jiya suna shagulgula, hankalin al'ummar kasar ta Senegal ya kwanta kasancewa rikicin siyasar ya zo karshe, tuni ma al'amura sun fara komawa yadda aka saba.

Sai dai kuma jama'a da dama sun zaku su ga irin kamun ludayin zababben shugaban kasa Macky Sall.

A farkon wata mai zuwa ne dai za a rantsar da sabon shugaban kasar, wanda ya samu goyon bayan kawancen jam'iyyun da a wani lokaci daban ke adawa da shi saboda dai a kawar da Mista Wade, ya kuma yi alkawarin tabbatar da cewa an kayyadewa shugaban kasa wa'adin mulki biyu.

"An samu sakamakon zaben da aka gudanar, kuma al'ummar Senegal ne suka yi nasara. Zan kasance shugaba ga dukkan jama'ar Senegal don kuwa wannan zabe ya nuna irin bukatar al'ummarmu", in ji Mista Sall.

A karshe dai aniyar Shugaba Abdoulaye Wade ta sake yin takara don darewa kujerar shugaban kasa a karo na uku ta ci kasa bayan da al'ummar kasar sun zabi yin amfani da akwatin zabe a matsayin hanya mafi inganci ta raba shi da kujerar.

Ko da yake masu sa ido a kan zaben sun ce an samu kurakurai nan da can, ba tantama al'ummar Senegal sun yi magana da babbar murya, kamar yadda Tijs Berman, shugaban tawagar masu sa ido ta Tarayyar Turai ke cewa:

"An samu 'yar tawaya a wannan zabe, lallai ne mu bayyana hakan. Sai dai kuma baya ga wannan 'yar tawaya tsarin zaben gaba daya sahihi ne kuma ka iya cewa lallai wanda aka ce ya yi nasara ne ya lashe shi; wannan ba ko tantama".

Tun bayan samun mulkin kai dai ba a yi juyin mulki a Senegal ba, kuma mutane da dama sun yi ta fargabar cewa za a kare da munanan tashe-tahsen hankula.

Abubuwan da suka faru kwanan nan a Mali mai makwabtaka da kasar ta Senegal, inda sojoji suka yi juyin muliki, alamu ne da ke nuna irin raunin da tsarin dimokuradiyya ke da shi a yankin.

A Guinea kuma, wadda ita ma take makwabtaka da Senegal, 'yan adawa sun bayar da sanarwar kauracewa zagaye na biyu na zaben shugaban kasa saboda zargin aikata kazamin magudi.

Duk da kwarin gwiwar da yake da shi cewa zai lashe wannan zabe, ba abin da ya saura ga Shugaba Abdoulaye Wade, daya daga cikin shugabanni biyu da suka fi tsufa a nahiyar Afirka, illa ya rungumi kaddara, ya kuma tabbatar da mika mulki cikin lumana.

Mutane dai na shagulgula ne hade da ajiyar zuciya cewa a karshe dimokuradiyya ta yi nasara, sai dai wasu da dama na fatan ya isar da sako cewa za a iya kaucewa watannin da ak kawse aana ta da jijiyoyin wuya da kuma zub da jini.

Karin bayani