Obama ya nemi a karfafa tsaron sinadaran nukiliya

Hakkin mallakar hoto NA
Image caption Shugaba na jawabi ga shugabanin sama da kasashe hamsin

Shugaba Obama na Amurka ya yi kira ga kasashen duniya su karfafa hadin kai a bangaren kare duk wata barazana ta harin ta'addanci na nukiliya a farkon taron kolin da aka bude game da tsaron nukiliyar a Korea ta Kudu.

Mr Obama ya gaya ma Shugabannin kasashe sama da hamsin cewar sha'anin tsaro na duniya ya dogara ne da matakan da za su dauka a wurin taron.

Ya ce ana iya amfani 'yan makaman nukiliyar dake hannuwan da ba su dace ba a kashe daruruwan dubban mutane.

"Akwai haryanzu akwai wasu miyagun mutane da dama da ke neman sinadaran nukiliya, kuma ba zai iya daukan lokaci mai tsawo ba wajen amfani da su domin kashe daruruwan mutane.

"Kasashe da dama sun hallara a taron ne domin su dau mataki ba wai sun tattauna kawai ba. Saboda taron nan, zamu samu damar kare lafiyar mutane da dama." In ji Obama

Koda yake taron kolin ya maida hankali ne a kan ta'addanci da makaman nukiliya, ya zo ne a daidai lokacin da kasashen duniya ke nuna damuwa ga shirin nukiliya na Korea ta Arewa da Kasar Iran.