Rikicin Sudan da Sudan ta Kudu ya rincabe

Omar al-Bashir Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Omar al-Bashir na Sudan

Rikici tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu ya kara kamari a rana ta biyu a jere.

Sudan ta Kudu ta ce sojojin saman Sudan sun kai hari a kan wata rijiyar mai da ke kan iyakar kasashen biyu; har yanzu dai ba a tantance irin barnar da harin ya yi ba.

Rijiyar dai tana da muhummanci ga Sudan saboda kudaden shigar da take samar mata.

Wannan dai ita ce sa-insa mafi muni tsakanin kasashen biyu tun bayan da Sudan ta Kudu ta samu 'yanci daga Sudan a watan Yulin Bara.

Wakilin BBC a Khartoum y ace ga alamu fadan ya auku ne a wani yanki da kasancewa duniya suka amince cewa a cikin Sudan yake.

Hukumomi a Khartoum sun ce an soke ziyarar da aka shirya Shugaba Omar al-Bashir zai kai Sudan ta Kudu.

Karin bayani