An dasawa wani dan Amurka sabuwar fuska

Hakkin mallakar hoto AFP

Likitoci a Amurka sun dasa ma wani dan kasar sabuwar fuska da hakora da harshe da muka-muki a wata tiyatar canza fuska da suka ce ita ce ta fi kowacce wahala da aka taba gudanarwa.

Mutumin mai suna Lee Norris ba ya fita cikin jama'a tun lokacinda aka baata fuskar taasa a wani harbi da aka yi masa da bindiga shekaru goma sha-biyar da suka wuce.

Likitoci dai sun ce a yanzu yana murmurewa bayan wannan tiyata da aka shafe awoyi talatin da shidda ana yi masa cikin makon jiya, a yanzu haka ma har an ce ya wanke bakin na sa da magogi ya kuma yi gyran fuska.

Dr Eduardo Rodri-guez ya bayyana abinda Mr Norriss din ya yi a karon farko da ya kalli fuskar ta'a sa a madubi:

Ya ce; "Ya ajiye madubin a kasa, ya yi mini godiya, ya rungume ni."