Sojin Mali sun fito da sabon kudin tsarin mulki

Hakkin mallakar hoto x

Shugabanin mulkin Soji a kasar Mali sun ba da sanarwa cewar za su yi aiki da wani sabon kundin tsarin mulki.

Sun bayyana hakan ne jim kadan bayan kungiyar raya tattalin arzikin yankin watau ECOWAS ta dakatar da kasar daga cikin kungiyar samakon juyin mulkin da sojojin suka yi a makon da ya wuce.

A sanarwar da suka bayar ta gidan talabijin, sojojin sun yi alkawarin ba da 'yancin bayyana ra'ayoyi da walwala

Gwamnatin Mulkin Sojin dai ba su yi wata magana ba a kan ko za su sake maido da gwamnatin da suka hambaras kamar yadda makwabtan kasar ta Mali suka nema.

Tun farko dai a wani taron koli na gaggawa na kungiyar ta ECOWAS, ta ba da sanarwa cewar ta sanya dakarun yankin su zauna ciikin shirin ko-ta-kwana.

Kungiyar ta ECOWAS ta ce akwai karin wani jeri na takunkumi da za su saka ma kasar, da kuma yiwuwar amfani da karfin soji idan har Shugabannin Sojin na Mali suka yi watsi da kiraye-kirayen kungiyar.