ECOWAS ta yiwa shugabannin sojin Mali barazana

Masu Zanga zanga a Mali Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Masu Zanga zanga a Mali

Hambararren shugaban Mali Amadou Tounani Toure ya ce yana nan a Bamako babban birnin kasar, kuma yana cikin koshin lafiya.

Tsohon shugaban bai bayyana inda yake ba, kuma yace baya hannun sojojin da suka kifar da gwamnatin sa a makon jiya.

Dubban 'yan kasar ne suka yi maci dazu a Bamako don nuna goyon bayan su ga sabuwar gwamnatin sojin kasar. Sun rera wakokin da a ciki, suka yi Allah wadai da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika, ECOWAS data dakatar da kasar.

Kungiyar ta ECOWAS tace a shirye take ta yi amfani da karfin soji da kuma takunkumi don kawadda sojojin

Tun farko Shugabannin mulkin sojin Mali sun ce za su fara aiki da wani sabon kundin tsarin mulkin kasa, jim kadan bayan kungiyar raya tattalin azrikin kasashen yammacin Afrika ta takakarda ita saboda juyin mulkin da suka yi a makon jiya.

A Wani jawabi ta gidan telbijin, sojojin sun yi alkawarin mutunta, 'yancin fadin albarkacin bakin jama'a da kuma walwala.

Sai dai babu batun lokacinda za a mika mulki ga gwamnatin da aka hambararr.

Shugaban Ivory Coast, Alassan 0uatara yace ya shaidawa wata tawagar sojojin da taje kasar sa cewa dole ne a dawo da tsarin dimokiradiyya.

A taron gaggawa da aka yi, kungiyar ECOWAS tayi shellar cewar zata aike da wata tawaga zuwa kasar Mali , wadda dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar zasu mara ma baya.

Shugaban hukumar ECOWAS, Kadre Desire Querdarogo yace "taron ya bada izini ga dakarun kungiyar akan su kasance cikin shirin ko ta kwana . Idan shugabanin soja na kasar Mali sun ki yin biyaya akan shawarar da aka yanke".

Matsayar da kasashen yammacin Afrika suka cimma ta kasance manuniya akan abubuwan da suka faru a watan Junairun bara.

A wancan lokacin dai Laurent Gbagba ya ki sauka daga kan karagar mulki bayan ya sha kaye a zaben shugaban kasar Ivory Coast da aka yi.

Haka zalika a wancan lokacin shugabannin yankin sunyi balaguro zuwa Ivory Coast kuma sunyi barazanar amfani da karfin soja.

Karin bayani