Fafaroma ya gana da Fidel a Cuba

Fafaroma da Fidel a Cuba Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Fafaroma da Fidel a Cuba

Fadar Vatican tace Fafaroma Bendict ya gana da tsohon shugaban Cuba Fidel Castro.

Kawo yanzu dai babu karin bayani a kan taron wanda yazo a karshen wata ziyarar kwanki ukku da Fafaroman keyi a kasar ta Cuba.

Fidel Castro ya shedawa Fafaroman cewar yana kallon yadda gidan Talabijin ke watsa bayanan ziyarar ta sa zuwa Cuba.

Tun farko dai mutane kusan dubu ukku ne suka halarci addu'in da Fafaroman yayi a dandalin yujin zuya halin Birnin Havana, inda ya yi kira ga 'yan kasar dasu nemi abunda ya kira sahihin 'yan ci.

Karin bayani