Kasashen yammacin duniya na kokanto akan Assad

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban Syria, Bashar Al Assad

Kasashen Yammacin duniya sun yi kokanto da jin cewar gwamnatin Syria ta amince da shirin zaman lafiyar da Kofi Annan wakilin musamman na kungiyar kasashen larabawa da Majalisar Dinkin Duniya ya gabatar.

An gabatar da shirin zaman lafiyan ne da nufin kawo karshen tashin hankalin da ake yi a kasar.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta ce Shugaba Assad yana da tarihi da yin alkawurra amma kuma ba ya cikawa.

Ta ce dole ne gwamnatin Syria ta dakatar da bude wuta, tare da ba da kafar kai agaji ga masu bukata, yakamata kuma ta fara shirin zabe na democradiyya.

Wannan shiri na Mista Annan shine shirin farko na kawo karshen rikicin da ake yi a Syria wanda ya samu goyon bayan dukkan wakilai a kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya.

'Yan adawa

Wakilai daga kungiyoyin adawa dabam-dabam a Syria sun amince da Majalisar kasa ta Syria a matsayin karbarbiyar gwamnatin a Syrian da za ta rika wakiltar al'ummar kasar, bayan wani taro da 'yan adawa su ka yi a birnin Santabul na hada kan 'yan adawar kasar.

Majalisar Kasa a Syria a kafa ta ne a watan Satumban bara, kuma ita ce ke tattaunawa da kasashen duniya kan rikicin na Syria, amma kungiyoyin fararen hula a cikin Syria na sukar Majalisar da cewa ba ta tasiri wajen magance rikicin na Syria.

An dai dauki kusan kwanaki biyu ana tattaunawa tsakanin 'yan adawa domin amincewa su fito karkarshin lema guda, abun da kuma ya hada kungiyoyi da ke da tsau-tsauran ra'ayin Islama da masu ra'ayin gurguzu.

A lokacin taron ma, sai da su ka nuna banbanci ra'ayoyin da ke tsakaninsu, abun da kuma yasa wasu kalilan da ga cikinsu suka fice a taron, wasu kuma su ka soki, shugabanin Majalisar 'yan adawa a fili.

Kwarin gwiwa

Amma daya daga cikin shugabanin Kungiyar Bassma Kodmani ta ce tana ganin an samu muhimmin ci gaba a fafutukar da su ke yi.

"Ya kamata mu rika karawa kasashen duniya kwarin gwiwa musamman ma wadanda ke nuna goyon baya ga fafutukar da muke yi a Syria,"

"kuma wannnan kungiyar ce za ta yi issar da sakon ga al'ummar kasar, kuma ina ganin kungiyar Majalisar 'yan adawa tana goyon bayan al'ummar Syria." In ji Kodmani.

Abu daya da 'yan adawan su ka amince da shi gaba daya, shine shakkun da su ka nuna, game da amincewar da Shugaba Assad ya yi da shirin zaman lafiya da wakilin Majalisar Dinkin Duniya, Mista Kofi Annan ya gabatar, inda suka ce basu yarda Shugaba Assad da gaske yake ba.

Shirin dai na neman a tsagaita wuta sannan kuma a tattauna a kan makomar Syria.

Shirin dai bai fayyace cewa ko Shugaba Assad zai sauka daga kan mulki ba, abun da kuma 'yan adama ke nema kuma sun ce zaman lafiya ba zai samu ba a kasar, muddin Shugaba Assad bai sauka daga kan mulki.