Wani limamin Vatican ya tattauna da Musulmai a Abuja

pope Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Papa Roma Benedict

Domin wanzar da fahimtar juna da samar da maslaha tsakanin mabiya addinin musulunci da na kirista a Najeriya, a yau ne wani limamin addinni kirista dan darikar katolika ya je najeriya daga fadar Vatican, domin tattaunawa da shugabannin addinin musulunci na kasar.

Jean Louis Cardinal Tauran wanda shi ne shugaban majalisar tattaunawa tsakanin addinai a fadar ta Vatican ya je Najeriyar ne domin fahimtar irin dangantakar da ke tsakanin mabiya addinan biyu a kasar.

Najeriya dai ta da de tana fama da matsalar rikice rikicen da ake dangantawa da addini.