Shugabanin kasashen ECOWAS za su je Mali

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Gbagbo da Jami'an ECOWAS

A yau ne ake saran wasu Shugabannin kasashen kungiyar yammacin Afrika ECOWAS ko CEDAO wadanda suka hada da shugaban kasar Codevoir da Burkina Faso da Benin da Liberia da Nijar da kuma Najeriya zasu je kasar Mali a yunkurin da suke yi na ganin sun mayar da kasar kan turbar democradiyya.

Hakan kuwa ya biyo bayan shawarar da Shugabannin kungiyar suka cimma ne a taron da suka gudanar ranar talata a kasar ta Côte d'Ivoire.

Ita dai gwamnatin mulkin sojin ta Mali, na cigaba da fuskantar matsin lamba a cikin gida da kasashen waje a kan bukatar ganin sun mika mulki ga farar hula.

Karin bayani