An saki Agaly Alambo a Jamhuriyar Nijar

Agaly Alambo Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban tsohuwar kungiyar 'yan tawaye ta MNJ, Agaly Alambo

A Jamhuriyar Nijar, kotu ta yiwa shugaban tsohuwar kungiyar 'yan tawaye ta MNJ, Agaly Alambo, sakin talala.

An dai tuhumi Agaly Alambo ne da hannu a safarar makamai tare da wani tsohon dan tawaye, Abta Hamdi Mohamed, wanda ke daure a gidan yari tun cikin watan Yunin da ya gabata.

Mai Magana da yawun kungiyar ta MNJ, ya shaidawa BBC cewa kotun ta saki Alambo ne ba tare da gitta masa wani sharadi ba.

Ya kuma kara da cewa “Tun ran da muka ajiye makamai muna nan a kan [bakanmu na] tabbatar da zaman lafiya [saboda] fitina bat a amfanar kowa—bat a amfanar Nijar, bat a amfanar wadanda suk dauki makamai”.