Paparoma ya bukaci 'yancin addini a Cuba

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Fidel Castro da Paparoma

Paparoma Benedict yayi kira ga Kasar Cuba da ta gina sabuwar al'umma mai kyawun makoma, wacce ta hada kowa da kowa, inda kuma adalci da 'yanci suke wanzuwa.

Wadannan bayanan dai sun zo ne a karshen ziyarar kwanaki ukun da ya kai kasar, inda Paparoman yayi kira ga 'yan Cuban da su nemi 'yanci ingantacce.

Paparoma Benedict ya yi amfani da lokacinsa a Cuba don jan hankalin tsibirin zuwa ga sauyi. Ya jaddada batutuwa kan mulki da jin raayoyin jamaa da sabuntawa da kuma adalci. Sannan kalamansa na karshe daf da zai tafi na da karfin gaske inda yake cewa adalci na da mahimmanci ga mutanta dan Adam.

wannan kalaman na da da ci ga gwamnatin Cuba da ke mulkin gurguzanci mai Jamiyya daya tilo, inda sauyi na tattalin arziki ke tafe amma ba bu batun sauyi kan siyasar kasar.

Wani batu kuma shine sukan da Paparoma yayi ga tsarin Amurka, wato takunkumi na kasuwanci na kusan shekaru hamsin da Paparoman yace ya kakabawa yan Cuban wani nauyi mara adalci.

Da farkon wayewar gari dandazon mutane ne suka yi dafifi a dandalin juyin juyi hali. Kafin ya bar garin Paparoman ya gana da Fidel castro na kusan rabin saa a wani taro da Vatican ta bayyana shi a matsayin taron samun jituwa da kuma amfani.

Karin bayani