Yan sandan Faransa sun kama musulmai 20

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban kasar faransa Nicolas Sercozy

'Yan sandan Faransa dake bincike kan dan bindigar nan Mohammed Merah sun kama akalla wasu musulmi su ashirin da suke zargi, a kudu maso yammacin garin Tolouse.

An dai kashe Muhammed Merah wanda ya kashe mutane bakwai a harbe- harbe daban daban, bayan da akaiwa gidan da yake ciki kawanya a makon daya gabata.

Kamun sanyin safiyar da akayi a Tolouse da Nantes na daya daga cikin binciken samo wadanda suka hada baki wanda aka ganshi da Mohammed Merah da dan uwansa kafin yayi harbin.

jamian tsaro na sirri ne na cikin gida suka gudanar da kamen DCRI da taimakon Jamian 'yan sanda da ake kira Farmaki.

Karin bayani