Shugabannin sojin Mali sun nemi taimako

Sojojin Mali Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugabannin sojin Mali sun nemi taimakon kasashen waje don murkushe boren Azbinawa

Shugaban sojojin da suka bijire suka kwace iko a Mali a makon da ya wuce ya bukaci taimakon kasashen waje don murkushe boren Azbinawa a arewacin kasar.

Kyaftin Amadou Sanogo ya shaidawa wani taron manema labarai cewa sojoji na bukatar taimakon kawayensu don kare martabar kasar ta Mali.

Kyaftin Sanogo ya yi magana da 'yan jaridar ne yayinda Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma, wato ECOWAS, ta ayyana wani shiri na matsawa kasar ta Mali lamba muddin shugabannin juyin mulkin ba su kiyaye suka kuma sake mika mulki ga farar hula a cikin lokaci ba.

Ya yi rokon nasa ne yayin da aka bayar da sanarwar cewa 'yan tawayen Azbinawan sun kwace garin Kidal mai muhimmanci.

Shaidu sun ce dakarun gwamnati sun gudu daga wuraren da suka ja daga a can cikin sa'o'i ashirin da hudu bayan da 'yan tawayen suka fara yiwa garin luguden wuta.

Karin bayani