Manoma na Korafi kan raba taki ta salula

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption shugaba Jonathan

Manoma sun fara tofa albarkacin bakinsu kan sabon shirin gwamnatin Najeriya, na rabawa manoma taki ta hanyar amfani da wayar salula.

Manoman dai na korafin cewa sabon tsarin kan iya kawo cikas ga ci gaban aiyukan noma, saboda wasu manoman dake Kauyuka basu da ilimin sarrafa wayar salula.

A wancan Tsohon tsarin dai, manoman sun koka game da abinda suka kira baba- keren da 'yan siyasa ke yi wajen rabon takin, inda ainihin manoma ke korafin takin ba ya isa garesu.

Manoman na cewa akwai wadanda a cikinsu ba su da wayar; basu kuma da ilimin sarrafa wayar. wasu kuma da suke da ita wayoyin na kasancewa a rufe saboda karancin wutar lantarki.

Karin bayani