Amurka tana shirin karawa Iran takunkumi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Obama da Medvedev

Kasar Amurka tana shirin sakawa Iran karin ta kunkumin mai, saboda shirinta na Nuclea.

shugaban kasar Amurkan Barak Obama ya fitar da wata takarda, yana mai cewa akwai isasshen mai a duniya da zai bada damar rage sayen man Iran.

Ta kunkumin dai da Kasar Amurkan ke shirin karawa kan kasar Iran yunkuri ne na kara matsin lamba kan shirin da Iran takeyi na Nuclear don yi mata barazana.

Bayan watan Yuni kasashen da suka sayi mai ta babban bankin Iran za su fuskanci ta kunkumin kasar Amurka.

Karin bayani