Mutum daya ya hallaka a rikicin Jos

Image caption Jamii'an tsaro a Jos

Rahotanni daga karamar hukumar Riyom ta Jihar Plato na cewa an kona gidajen fulani fiye da guda ashirin a yau kana aka kashe mutum guda.

Fulanin dai na zargin jami'an tsaro ne da aikata hakan bayan wasu rahotanni dake cewa an kashe wani dan sanda a yankin.

Kakakin rundunar yansandan jihar ta Plato ya tabbatar da faruwar lamarin wanda yace ya biyo bayan kashe wani dan sanda ne amma ya ce bashi da tabbacin ko jamiansu ne suka yi kone kone.