Mali: 'ba zamu dawwama akan mulki ba'

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kaftin Amadou Sonogo, shugaban mulkin sojan Mali

Sojojin da suka kwace mulki a kasar Mali sun ce ba su da niyyar dawwama kan karagar mulki, kuma zasu bar fagen mulkin da zarar aka warware rikicin kasar.

Daya daga cikin wadanda suka yi juyin mulkin, Kanar Musa Coulibaly, bayan halartar wata tattaunawa a kasar Burkina Faso makwabciyar su, ya ce ba su da niyyar yin babakere a kan mulki.

A Bamako, babban birnin kasar, dubban jama'a daga kungiyoyin addinai daban daban sun yi gangami na kiran a warware rikicin cikin lumana.

Karin bayani