Masu ra'ayin rikau na gangamin kyamar musulunci

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jean Claude

Kungiyoyi masu ra'ayin rikau a kafatanin Nahiyar Turai za suyi wani gangami a Denmark yau Asabar don samun hadin -gwiwa na kyamar addinin Islama a Nahiyar.

Kungiyar masu ra'ayin rikau na English Defence League ( wato masu ra'jin kare Ingilishi) ne suka hada zanga zangar.

Kungiyar ta ce tana son ta dakatar da abun da ta kira musuluntar da Nahiyar Turai.

wasu tuni sun isa birnin Danish na Aarhus tun ranar Laraba inda suka samu damar yin taro da tattaunawa kan mura dansu.

Masu kamfe kan wariyar launin fata na cewa kungiyoyin masu raayin rikau sun samarda sako a lokacin da ake fama da wahalhalun durkushewar tattalin arzuki.

Karin bayani