Burtaniya ta jaddada goyon baya ga Falklands

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Firai ministan Burtaniya, David Cameron

Firai ministan Burtaniya David Cameron ya jaddada goyon bayan kasar ga al'ummar tsibirin Falklands a lokacin tuna cika shekaru talatin da mamayar da kasar Argentina ta yi ma tsibirin na falklands.

Mr. Cameron ya jinjina ma sojojin Burtaniya da aka tura su sake kwato tsibirran tare da nuna alhininsa ga mayakan Brittaniyar da Argentina da suka rasa rayukkan su a yakin Falklands din da aka shafe makonni shidda ana gwabzawa.

Sharon Halfords shugabar majalisar dokoki ta yankin Falklands ta bayyana cewar mutanen tsibirran baa shagulgulan mamayar da aka kai musu suke yi ba, suna tuna wani lokaci ne, wanda dole suka kaare kansu.

'Yan kasar ta Argentina da suka yi wancan yakin sun shafe daren jiya suna addu'oi a tashar jiragen ruwa ta Ushu'ai dake kudancin kasar a wurinda aka jibge sojoji lokacin mamayar.