Gwamnatin Kano za ta kafa Jami'a ta arewa masu yamma

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Gwamnatin jihar Kano a arewacin Nigeria ta ce ta samu izinin kafa wata sabuwar Jami'a ta arewa maso yamma a jihar.

Gwamnatin tace zata samar da jami'ar ne don rage matsalolin rashin samun gurabe a jami'o'i da 'yan asalin jihar ke fama da su yanzu haka.

Jami'ar dai da aka yiwa lakabi da jami'ar Arewa maso yamma zata fi maida hankali wajen daukan dalilabai 'yan shiyyar arewa maso yammacin kasar, yankin da ya kasance koma baya a kasar ta fuskar ilimi.

Samar da sabuwar jami'ar dai na zuwa ne a daidai lokacin da jami'ar Kimiyya da fasaha ta Jihar dake Wudil ke kokarin tsayawa da kafafuwanta.

Wasu dai na ganin gara a maida hankali a kanta Jami'ar ta Wudil kafin a samar da wata.