Mutane 43 sun rasu a hadarin jirgin sama a Siberia

Hakkin mallakar hoto AP

Wani jirgin saman fasinja na kasar Rasha dauke da mutane arba'in da uku ya fadi a Siberia.

Ma'aikatan ceto sun ce mutane a kalla talatin da daya dake jirgin suka mutu a yayinda aka kwashi da dama da suka tsira zuwa asibiti.

Jirgin saman kirar Faransa ATR-72 wanda kamfanin sufurin jiragen saman Rasha Utair ya yi amfani da shi a jigilar fasinjan ya tashi ne daga filin jiragen sama na Tyumen zuwa Surgut na arewa maso gabashin kasar.

Jirgin dai ya bace a na'urar hangen jiragen saman kafin ya fadi.