'Yan tawayen FARC sun saki mutane 10 a Columbia

Yan tawaye na kungiyar FARC a Columbia sun saki mutane goma na karshe da suka hada da 'yan sanda da sojoji wadanda suka yi garkuwa da su a wani aiki da aka yi a karkashin kulawar kungiyar ba da agaji ta Red Cross.

An yi amfani da karamin jirgin sama wajen kwaso mutanen da aka yi garkuwar da su daga kurmi na kasar ta Columbia.

Hotunan Talabijin sun nuno mutanen da aka yi garkuwa da su a filin jiragen sama na Villa-vicencio wurinda suka hadu da iyalansu bayan shafe sama da shekaru goma a tsare.

Ana kyautata zaton dai har yanzu 'yan tawayen na kungiyar FARC suna rike da daruruwan farar hula.

Shugaban kasar Colombia Juan Mauel Santos ya yi marhabin da sakin 'yan sandan da sojoji goma.

Amma yace karimcin kungiyar 'yan tawayen ta FARC har yanzu bai isa ba.

Ya bukaci a sako farar hular da har yanzu ake tsare da su, ya kuma ce gwamnatinsa za ta ci gaba da manufar ta, ta fuskantar kungiyoyin masu gwagwarmaya da makamai.

Msta Santos din ya gode ma kasashen da suka taimakawa a kawo karshen rikicin da aka shafe shekaru hamsin ana gwabzawa.

Ya ce batun zaman lafiya wani abu ne da ya rataya ga wuyan 'yan kasar ta Colombia.