Mayakan sa -kai sun kafsa a Libya

sojin Libya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption sojin Libya

Hukumomi a Libya sun ce fadan da ake yi tsakanin wasu mayakan sa-kai wadanda ba sa ga maciji da juna ya hallaka mutane 14 yayinda akalla takwas suka jikkata a arewa maso yammacin kasar.

Ana ba-ta-kashin ne dai a kusa da garin Zuwara, wanda akasarin mutanensa 'yan kabilar Berber ne, inda ake ta samun tashe-tashen hankula tun bayan kifar da gwamnatin Kanar Gaddafi a watan Oktoban da ya gabata.

Wakilin BBC ya ce ministan harkokin wajen Libya ya ba da sanarwar za a aike da jami'an tsaro dari biyu don su maido da zamna lafiya a yankin.

Daya daga cikin manyan kalubalen da Majalisar rikon Kwaryar kasar ta Libya ke fuskanta shi ne yadda za ta yi iko da mayakan sa-kan da suka kifar da Gaddafi, wadanda ba sa ga-maciji-da juna.

Karin bayani