Sojojin Mali na kamun kafa da Najeriya

Jagoran sojin Mali Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jagoran sojin Mali

Gwamnatin mulkin Sojan Mali sun tura wata tawaga ta mutane uku don tattaunawa da ministan harkokin kasashen wajen Najeriya, Olugbenga Ashiru.

Jagoran tawagar Kanal Blonkero Samake wanda yayi jawabi da harshen Faransanci kafin su shiga taro na sirri, ya ce zun je su yiwa hukumomin Najeriya bayani ne game da halin da ake ciki a Mali.

Kungiyar kawancen tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma ECOWAS ta sanya takunkumin tattalin arziki akan kasar ta Mali, bayan juyin mulkin da sojojin suka yi kusan kwanaki goma da suka gabata.

A waje daya kuma a Najeriyar yau wata gammayar kungiyoyin fararen hula na kasashen yammacin Afrika suka yi wata zanga zangar nuna rashin amincewa da juyin mulki soja a ofishin jakadancin kasar Mali dake birnin Abuja .

Masu zanga zangar sun yi kira ga gwamnatin soja Mali akan su mika mulki ga farar hula ba tare da bata lokaci ba.

Karin bayani