Boko Haram kungiyar ta'addanci: Inji 'yan Majalisa

Jagoran kungiyar Boko Haram Hakkin mallakar hoto youtube
Image caption Jagoran kungiyar Boko Haram

Wasu yan majalisar wakilan Amurka biyu sun yi kira ga hukumomin Amurakar da su dauki kungiyar Jama'atu Ahlissunna Lidda'awati wal Jihad ko kuma Boko Haram ta Najeriya a matsayin kungiyar ta'addanci.

Kiran na yan majalisar ya zo ne bayan da wani babban jami'in diplomasiyyar Amurka ya yi gargadin cewa a ringa lura da kungiyoyin yan ta'dda, inda yace kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayin Islama, ba wasu manyane na azo a ganiba, sannan kuma matsaloli na cikin gida sune suke haifar dasu.

'Yan Majalisar peter King da Patrik Meehan sun ce kungiyar ta Boko Haram da ta dauki nauyin kai hare hare a Kano ranar 20 ga watan Janairun bana da suka janyo mutuwar kimanini mutane 200 na kara bunkasa kamar yaddda kungiyar Taliban a Pakistan da kuma kungiyar Alqa'ida a kasar Yemen suka fara.

A wata wasika da suka aikewa sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton, 'yan majalisar 'yan jam'iyyar Republican sun ce dole ne Amurka ta dau batun da mahimmanci sannan kuma kada hukumomin kasar su yi sake wajen tunkarar gagarumin barazanar ta'addanci dake tattare da kungiyar.

'Yan majalisar suka ce kwarewa wajen hare haren da kungiyar ta ke kaiwa da suka hada da na ofishin majalisar dinkin duniya a Abuja cikin watan Agustar bara, dana cocin sen Trazer a Madalla dake suleja ranar Kirsimeti su na kama da na alqa'ida, abinda hakan ke nuna cewa kungiyar na da dangantaka da alka'ida.

Tun a baya ma dai shugaban kwamitin tsaron cikin gida na majalisar wakilan ta Amurka, King ya ta ba gargadi kan abinda ya ke cewa barazanar tsaro daga kungiyar ta Boko Haram, abinda har ya kai majalisar ta gudanar da wani zaman jin ra'ayi kan kungiyar ta Boko Haram a bara.

Ko a ranar Alhamis din makon jiya ma dai mataimakin sakataren harkokin cikin gida na Amurka mai kula da nahiyar Afrika, Johnnie Carson ya bayyana barazanar tsaro ta kungiyar ta Boko Haram ga Amurka da cewa ba ta wasa ba ce, sai dai bai karfafa cewa kungiyar tana da dangantaka da Alq'ida ba.

Sanya kungiyar dai ta Boko haram cikin kungiyoyin ta'addanci zai sa gwamnatin Amurka ta hana taba duk wata kadara ta kungiyar da 'ya'yanta, da kuma damar gurfanar da duk wani dan kungiyar.

Karin bayani