An nada Youssouf Ndour a matsayin Minista a Senegal

Hakkin mallakar hoto
Image caption Youssouf Ndour

A Senegal an nada shahararren mawakin nan Youssouf Ndour a matsayin Ministan al'adu da yawon bude ido.

Wanann dai ya biyo bayan rantsar da sabon shugaban kasar Makky Sall a ranar talata.

Ndour ya goyi bayan Mr Sall ne bayan kotun tsarin mulkin kasar ta dakile yunkurin da shi kansa ya yi na tsayawa takara.

Youssuf Ndour wanda ke da dimbin magoya baya a nahiyar Afrika ya yi wakar samun nasarar Mr Sall a gaban dubban mutane da suka hallara a babban dandalin taro na Dakar.

A dandalin ne dai magoya bayan 'yan adawa suka rinka kafsawa da jami'an tsaro a lokacinda ake yaakin neman zabe.