An yankewa 'yan sanda hukuncin dauri a Amurka

Hakkin mallakar hoto AFP

Wani alkali a Amurka ya yanke hukuncin dauri mai tsauri na shekaru gidan kurkuku ga wasu tsoffin jami'an 'yan sanda biyar.

An yankewa jami'an 'yan sanda hukuncin ne saboda rawar da suka taaka a harbe-harben da aka yi aka kashe mutane a New Orleans bayan mahaukaciyar guguwar nan ta Katrina a shekara ta dubu biyu da biyar.

'Yan sandan dai sun yi ta harbin farar hular da ba su da wasu makamai a kan gada inda suka kashe biyu daga cikin su.

Daga bisani don su fake a kan cewar sun dauki matakin ne a kan doka, mai gabatar da kara yace jami'an 'yan sandan suka yi makircin ajiye bindiga, sannan kuma suka sanya sheidun karya da kuma rubuta rahotannin karya.

Hudu daga cikin 'yan sandan dai an yanke musu hukuncin daga shekaru talatin da takwas zuwa sittin da biyar a gidan kurkuku, yayinda na biyar aka yanke masa hukuncin daurin shekaru shida saboda boye gaskiya da ya yi.