Mutane bakwai sun rasu a tashin bam a Somalia

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Wata fashewar da aka samu a wani sabon gidan wasan kwaikwayo a Mogadishu babban birnin Somalia, ta hallaka mutane bakwai tare da raunata wasu da dama.

Daga cikin wadanda suka rasu, harda shugaban hukumar kwallon kafar kasar da kuma shugaban kwamitin gasar Olympics na Somaliyar.

Fryministan kasar Abdiweli Mohammed Ali na daga cikin wadanda suke cikin sabon gidan wasan kwaikwayon lokacin da bam din ya tashi.

Ya shaidawa BBC cewar wata mace 'yar kunar bakin wake ce ta tada bam din.

Kungiyar 'yan gwagwarmaya ta Al Shabaab wacce ta dauki alhakin kai harin, ta soma amfani da kunar bakin wake ne tun lokacin da aka fatattaketa daga Mogadishu a watan Agustan 2011.

Karin bayani