Amurka ta tura mayakan ruwa dari 200 zuwa Austrailiya

Hakkin mallakar hoto AFP

Wani ayarin mayakan ruwan Amurka ya isa Australiya a karon farko.

Mayakan wadanda yawansu ya kai dari biyu sun isa birnin Darwin da ke arewacin kasar ne a wani yankuri na kara yawan sojin Amurka a yankin Pacific.

Shugaba Obama ya ce kara yawan sojojin wata dabara ce na yiwa China matsin lamba amma masu sharhi na ganin Amurka na so ta yi goggaya ne da China a yankin, musamman ganin irin tasirin da China ke yi a yankin na Pacific.

Mayankan ruwan Amurka dari biyu a yanzu haka, sannan kuma dubu biyu da dari biyar nan da shekaru biyu.

Wannan ne dai karo na farko da Amurka ta nuna kudirin sauya dakarun ta a Austrailiya na din-din-din.

Duk da dai yawan dakarun nata ba wani yawan yake da shi ba, wasu dai na ganin wani yunkuri ne da Amurka ke yi domin gogayya da China a yankin na Pacific ganin irin rawar ganin da kasar ke takawa.

A wata ziyara da ya kai Australia a bara inda ya bayyana cewa Amurka za ta kara yawan dakarun ta a yankin Shugaba Obama ya bada tabbacin cewa ba wai Amurka na nema ta mamaye ayyukan da China ke yi a yankin bane, Amma sai dai wasu manyan jami'an gwamnatin China sun nuna damuwa ga ayyukan sojin Amurka a yankin.

Ganin cewa Amurka na da sansanin Soji a kasar Korea ta kudu da Japan da ma wasu wurare a yankin na Pacific, China ta nuna damuwa ga karin sojin da Amurka ke yi a yankin, abun da kuma ta ce tana ji ne kamar ana mamaye ta ne.

Ministan tsaron Australia, ya bayyana cewa Amurka ta kara yawan sojin ta ne a yankin saboda ta samu karfin fada a ji ne a yankin ganin irin tasirin da China da kuma Indiya su ke yi a harkar siyasa da kuma tattalin arziki a yankin.

Mayakan ruwan na Amurka da su ka isa Darwin za'a yi amfani da su ne wajen ayyukan agaji a yankin na Pacific.