Birtaniya ta yi gargadi kan Boko Haram

Boko Haram Hakkin mallakar hoto youtube
Image caption Malam Abubakar Shekau, Jagoran Boko Haram

Birtaniya ta gargadi 'yan kasarta da su guji wasu jihohi bakwai na arewacin Najeriya saboda wata babbar barazanar kai harin ta'addanci a lokacin bukukuwan Easter.

Ma'aikatar harkokin wajen Birtaniya ta sabunta gargadin nata ne, tana mai cewar kungiyar masu tsattsauran kishin Islama a Najeriya da ake kira Boko Haram ta kai hare hare a ranar Kirsimatin da ya wuce, harin da yayi sanadiyar mutuwar mutane da yawa a wani Cocin Katolika a wajen Abuja Babban Birnin Tarayyar kasar.

Ma'aikatar dai ba ta bayar da wani karin cikakken bayani game da barazanar ta ranar Easter ba.

Sai dai Gwamnatin Amurka ma ta yi irin wannan gargadi ga 'yan kasarta game da zuwa Najeriyar.

To amma hukumomin tsaron Najeriyar sun musanta cewar akwai wata barazanar kai hari a lokacin Eastar.

Karin bayani