Najeriya: ana taro akan kasafin kudi

Goodluck Jonathan, shugaban Najeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Goodluck Jonathan, shugaban Najeriya

A Najeriya ana can ana tattaunawa tsakanin Shugaban kasa, Goodluck Jonathan da shugabannin majalisar dokoki ta kasa kan kasafin kudi na shekara ta dubu na bana.

Taron zai yi kokari ne na warware wani rashin daidaito ne da aka samu a kasafin kudin karshe da yan majalisar suka zartas.

Daya daga cikin bangarorin takaddamar shi ne farashin mai da kasafin kudin ya kunsa, wanda fadar Shugaban kasar ta ce 'yan majalisar sun kara shi daga Dola saba'in akan kowacce ganga guda zuwa dola saba'in da biyu.

A cikin watan Maris ne dai kasafin Kudin Najeriya na shekara ta 2011 ya kare.