An yankewa Bout hukuncin shekaru 25

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaba Obama

Dan kasar Rashan nan mai sayarda makamai wanda yayi kaurin suna, Viktor Bout ya koyi darasu daga zaman kurkuku da zaiyi na tsawon shekaru ashirin da biyar.

Wannan shine hukuncin da aka yanke masa bayan da ya amince ya sayarda makamai na miliyoyin daloli ga wasu da yake ganin cewa yan tawayen Colombia ne wanda za suyi amfani dasu wajan kashe matukan jirage masu saukar ungulu na kasar Amurka.

Sai dai Bout ya musanta zargin da ake masa inda ya yi ihu a kotun ya ce karya ne. Tsohon sojan Rashan an dana masa tarko ne. wadanda yake musu kallon yan tawaye ne; masu bawa Amurka bayanai ne.

Rahoton majalisar dinkin duniya dai na cewa makaman da ya ke samarwa ya haifar da fadace-fadace a Afruka. An kama Bout ne a Thailand kuma aka tusa keyarsa zuwa kasar Amurka don gur fanar dashi a gaban kotu.

Karin bayani