An tarwatsa masu zanga zanga a Bahrain

zanga zanga a Bahrain Hakkin mallakar hoto ap
Image caption zanga zanga a Bahrain

Jami'an tsaro a Bahrain sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye, da mesar feshin ruwa wajen tarwatsa dubban masu zanga zangar da suka yi cincirindo domin nuna goyan bayansu ga wani shugaban masu fafutukar kare hakkin dan adam.

Masu zanga-zangar sun rike hotunan mai fafutukar da ke kaso, Abdulhadi al-Khawaja.

Kusan kwanaki sittin kenan yana yajin cin abinci, yanzu kuma yana asibiti.

An ce rashin lafiyar da yake fama da ita ta kara tsananta, kuma kungiyoyin kare hakkin bil adama sun ce ya kusa mutuwa.

Mutumin ya daukaka kara ne kan hukuncin daurin rai da rai da aka yanke masa kan rawar da ya taka a zanga zangar kin jinin gwamnatin da aka yi ta yi a kasar bara.

Karin bayani