Ana tunawa da wadanda aka kashe a Bosnia

Kaburburan mutanen da aka kashe a yakin Bosnia Hakkin mallakar hoto afp
Image caption Kaburburan mutanen da aka kashe a yakin Bosnia

Ana gudanar da bukukuwan cika shekaru ashirin da yakin basasar da aka yi a Bosnia; daruruwan jama'a sun taru a Sarajevo, babban birnin kasar don yin bukukuwan.

Dubban mutane ne suka fito cikin ruwa don su saurari wakokin da ake ta yi a wajen.

An jera jajayen kujeru sama da dubu goma sha daya, wadanda aka yiwa wadansu daga cikinsu adon furanni, kowacce daya a matsayin mutum guda da aka kashe lokacin da dakarun sojojin Serbia suka yiwa Sarajevo kofar rago na dogon lokaci.

Akalla mutane dubu dari aka kashe a rikicin na Bosnia kuma an tilastawa kusan rabin al'ummar kasar barin gidajensu.