Oxfam ta ce ta kunkumin Mali zai mummunan tasiri

Image caption 'Yan ta-wayen Mali

Kungiyar bada agaji ta kasa da Kasa ta Oxfam tayi gargadin cewar takunkumin da aka kakabawa Kasar Mali zai yi mummunan tasiri.

A wata sanarwar da ta fitar, Kungiyar ta ce mutane sama da miliyan Uku ne suke cikin hatsarin kamuwa da yunwa, idan har ba a kula da bukatunsu ba.

Kungiyar tayi kira ga kasashen dake yankin dasu sake nazarin takunkumin, domin tabbatar da cewar an kare al'ummar Kasar.

haka kuma ta cigaba da laluben hanyoyin warware halin da ake ciki a kasar dake Afrika ta yamma.

Karin bayani