An ki amincewa da sabuwar kasar Azawad

'Yan tawayen MNLA a Mali Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan tawayen MNLA a Mali

Kungiyar Tarayyar Afrika (AU) ta yi watsi da shelar samun 'yancin da Azbinawa 'yan tawaye suka yi a arewacin kasar Mali, inda suka kwace iko.

Shugaban Hukumar Kungiyar ta AU, Jean Ping, ya ce sanarwar 'yanta yankin soki-burutsu ce kawai.

Mayakan Azbinawan dai sun yi ta kai samame suna karbe iko da garuruwa bayan rudanin da aka shiga sakamakon juyin mulki da sojoji suka yi a kasar Makwanni biyu da suka wuce.

A wata sanarwa da ta fitar ce dai Kungiyar Fafutukar Kwato 'Yancin Azawad (MNLA) ta nemi a amince da sabuwar kasar.

Daya daga cikin masu magana da yawun kungiyar a Paris, Moussa Aq Attaher, ya shaidawa BBC cewa suna neman goyon baya ne daga kasashen duniya:

“Da farko muna kira ga Majalisar Dinkin Duniya [ta amince da kasar], bisa tanade-tanaden dokokin kasa-da-kasa wadanda suka tabbatar da hakkin al'umma na cin gashin kansu, da kuma hakkin al'umma na samun gwamnatocin kansu, da kuma iko da yankunansu”, in ji Attaher.

Ya kuma kara da cewa, “Muna fatan samun goyon baya daga kasashe masu makwabtaka—wadanda suka shaida irin kisan kare-dangin da gwamnatin Mali ta rika yiwa al'ummar Azawad”.

'Yan tawayen da suka ayyana 'yancin-kan arewacin kasar ta Mali dai Abzinawa ne makiyaya.

Sai dai kuma abu ne mai wahala matuka kasashen duniya su amince da sabuwar kasar ta Azawad.

Tuni dai gwamnatocin kasashen Afirka masu makwabtaka da kasar ta Mali suka firgita saboda ballewar yankin ka iya zama darasi ga sauran 'yan tawayen da ke fadin nahiyar.

Sannan kuma Faransa, kasar da ta yiwa Mali mulkin mallaka, ta ce ’yan tawayen sun hada gwiwa da reshen arewacin Afirka na kungiyar Al-Qa'ida a gwagwarmayar tasu.

Shugaba Nicolas Sarkozy ya ce masu tsatstsauran ra'ayin Islaman na yunkuri ne na kafa abin da ya kira ‘kasar ’yan ta'adda’ a yankin.

Faransa dai ta yi alkawarin bayar da gudunmawar kayan aiki da shawarwari ga rundunar sojin da kasashen Yammacin Afirka ka iya kafawa da nufin kawo karshen rikicin na kasar Mali.

Karin bayani