Wani jirgin yakin sojin ruwan Amurka ya rikito a Virginia

Jirgin yakin Amurka na F18 ya rikito Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jirgin yakin na F18 ya samu matsala ne jim kadan bayan tashin sa.

Wani jirgin yakin sojin ruwan Amurka ya tarwartse a tsakiyar wani gari cikin jahar Virginia ta Amurkar, inda ya rusa wani gini ,sannan ya tada wuta akan wasu gine ginen .

Ma'aikatan jirgin na F18 su biyu dai sun wuntsulo, yayin da jirgin ya tuntsuro zuwa bakin ruwa a Virginia.

Akalla mutane biyar ne dai suka jikkata.

Wani wakilin BBC yace wani mutum daya taimakawa matukin jirgin yace matukin ya nemi afuwa saboda rusa masa gida.

Sojin ruwan dai sunce jirgin ya samu matsala ne jim kadan bayan tashin sa.

Karin bayani