Joyce Banda ta zama shugabar kasar Malawi

shugaba Joyce Banda ta Malawi Hakkin mallakar hoto
Image caption shugaba Joyce Banda ta Malawi

An rantsar da mataimakiyar shugaban Malawi, Joyce Banda a matsayin mace ta farko da zata shugabanci kasar bayan mutuwar wanda ya gabace ta Bingu Wa Mutharika.

Joyce Banda dai ta yi ransuwar kama aiki ne a wani buki da aka yi zauren majalisar dokokin kasar dake birnin Lolingwe.

An yi ta tafi da shewar taya ta murna.

Yayin wani wani gajeren jawabi da ta gabatar ta ce, zata gudanar da gwamnati mai inganci, kuma ta yi kira ga 'yan kasar ta Malawi da su hada kai.

Jinkirin sa'a ashirin da hudu kafin bayyana mutuwar Bingu Wa Mutharika ya sa an yi ta hasashen cewa, watakila akwai jayayya dangane da mulkin kasar.

Shekaru biyu da suka gabata ne dai aka kori Joyce Banda daga jam'iyya mai mulkin kasar.

Karin bayani