Sojin Mali sun amince su maida mulki ga farar hula

Keptin Amadou Sanogo na Mali Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugabannin da su ka jagoranci juyin mulki a Mali sun amince su sauka, su kuma maida mulki ga farar hula

Shugabannin da suka jagoranci juyin mulkin sojin Kasar Mali sun amince su sauka, su kuma maida mulki ga farar hula.

Shugaban sojojin da su kai wa gwamnatin Malin bore Keptin Amadou Sanogo ne ya bada wannan sanarwar.

Ana tsammanin Shugaban majalisar dokokin Kasar ne zai zama sabon Shugaban Kasar Malin na rikon kwarya.

Ministan harkokin wajen Kasar Burkina Faso, yace makwabtan Mali sun amince su dage takunkumin da suka kakabawa Kasar nan take

Karin bayani