Duhu na kawo cikas a aikin ceton dakarun Pakistan

dussar kankara a Pakistan Hakkin mallakar hoto AP
Image caption dussar kankara a Pakistan

Jami'ai a Pakistan sun ce, tsananin duhu da kuma rashin kyawun yanayi sun tilasta dakatar da aikin ceto dakarun kasar fiye da dari da ambaliyar dusar kankara ta rufta da su a wani sansani dake yankin Kashmir da ake takaddama a kansa.

Yayin da dare ya tsala, an samu cikas a aikin da ake na kokarin ceto wadanda lamarin ya rutsa da su.

Wakilin BBC ya ambaci kakakin rundunar sojan Pakistan na cewa, gobe da safe ne za a a ci gaba da aikin ceton, amma kuma an soma fidda kaunar samun wani a raye, a karkashin dussar kankarar.

Dama dai kawai dubban dakarun Pakistan din da kuma na India a wurin da lamarin ya auku.