Shugaban Yemen ya yi wa rundunar sojin Kasar garanbawul

Sabon Shugaban Yemen Abd Rabbu Mansour Hadi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban Yemen ya yi wa rundunar sojin Kasar garanbawul

Sabon Shugaban Kasar Yemen Abd Rabbuh Mansur Hadi ya sallami wasu manyan hafsoshin sojin Kasar su biyu da kuma wasu sojojin dake yiwa tsohon Shugban Kasar biyayya da dama, a wani mataki na farko na yin garanbawul ga rundunar sojin Kasar

Wadanda abin ya shafa sun hada da babban hafsan sojin saman Kasar Janar Mohammad Saleh Al Ahmar da kuma Shugaban jami'an tsaron fadar shugaban kasa Janar Tarik Muhammad Abdullah Saleh

Ana dai zargin tsohon Shugaban Kasar Ali Abdallah Saleh da amfani da masu yi masa biyayya wajen kawo rikici a Kasar.

Karin bayani