JTF ta Farma mafakar 'Yan Boko Haram

Image caption wajan da aka sa bam a najeriya

Rundunar tsaro ta JTF dake Maiduguri, a arewacin Najeriya, ta ce ta farma wadanda ake zargin yan Kungiyar Alhlul sunna lilda'awati wal Jihad da aka fi sani da Boko haram bayan bayanai da suka samu akan wurare da suke fakewa, inda a artabun suka kashe mutane uku suka kama biyu.

Rundunar ta ce ta killace wadanda ake zargin yan Boko Haram din ne a mafakarsu dake unguwar Bulabulin wanda ake zargin su ne suka kai farmaki a kasuwar Monday Market dake Maiduguri.

A farmakin dai na Monday market an kashe akalla mutane goma sha biyu an kuma yiwa wasu yan kasuwa fashi su biyar.

Lt Col Sagiru Musa kakakin rundunar JTF din ya ce sun samu bindiga AK 47 guda daya da Pistol guda biyu da kuma makamai daban daban guda 185.

Haka kuma sun ce sun gano wasu bama bamai da ba a tashe su ba a unguwar kwanar Yobe da misalin karfe uku da rabi na yammacin yau.

A cewarsa kwararru kan harkar bama bamai na rundunar sun kwance bama baman bayan da aka gano su.

Karin bayani