Bom ya tashi a Kaduna, anyi asarar rayuka

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption an kai hari a kaduna

Bom ya tashi a kan titin Ahmadu Bello way dake Jihar Kaduna inda yayi asarar rayuka da dama, wasu kuma suka jikkata.

Bayanai na cewa bom din ya tashi ne a kusa da wata mujamia, amma inda ya tashin bai kai wajan mujamiarba.

Sai dai tashin bam din ya zo ne adai dai lokacin da ake bukukuwan Easter.

Har izuwa yanzu dai hukumomi basu bada bayanai kan wadanda suka jikkata ba ko suka rasu.

Amma wani wanda ya ganewa idanunsa ya shaidawa BBC cewa ya ga gawa tara a inda bom din ya tashi.

Wadanda suka jikkata an kaisu asibitin Saint Gerrad Hospital.

Har izuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki nauyin kai harin.

Karin bayani